Kasar Chadi zata janye sojojinta daga Mali

Dakarun kasar Chadi
Image caption Dakarun kasar Chadi

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya ce za'a janye sojojin kasar daga Mali, da ke taimakawa dakarun Faransa dana Malin a yakin da suke yi da 'yan tawaye a arewacin kasar.

Shugaba Deby ya ce an kammala yaki na gaba da gaba da 'yan tawaye, inda ya bayyana cewa, sojojin kasarsa basu da kwarewa wajen yakin sunkuru.

Su dai sojojin kasar Chadin da aka tura Mali da yawansu ya kai dubu biyu, na daga cikin wadanda aka fi hallaka sojojinsu a yakin da ake yi da 'yan tawaye karkashin jagorancin sojojin Faransa.

Mr Deby wanda bai bayyana lokacin da za'a janye sojojin ba, ya ce kasar zata ba da sojoji da zaran an kammala shirye shiryen girke rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika.