An hallaka mutane sama da 20 a Iraqi

Hari a Bagadaza
Image caption Hari a Bagadaza

Wasu jerin hare hare da aka kai a daidai lokacin da jama'a suke rububin zuwa wuraren aiki a birane daban daban a kasar Iraqi yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 20 yayin da wasu sama da 180 suka samu raunika.

Ana jin yawan wadanda suka rasa rayukansu zai karu saboda munanan raunikan da wasu suka samu.

An bada rahoton cewa akasarin harin an kai ne a birnin Bagadaza. Sauran biranen da abun ya shafa sun hada da Fallujah da Kirkuk.

Hare haren sun zo ne a yayin da ake saura kwanaki biyar gabanin zaben larduna da za'a yi a matsayin zaben farko tun bayan da sojojin Amurka suka janye daga Iraqi a shekara ta 2011.

Wasu daga cikin wuraren da aka kaiwa harin sun shafi wuraren da za'a yi zaben ne.

An kashe yan takara 14 gabanin zaben.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare hare.

Karin bayani