Mutane 10 sun mutu a wani hari a kasar Iraqi

Wani jami'n tsaro a kasar Iraqi
Image caption Wani jami'n tsaro a kasar Iraqi

Mutane goma ne suka mutu a wani hari da aka kai a Iraqi, ciki har da wani dan takara a zaben lardunan da aka shirya gudanarwa a ranar asabar mai zuwa.

Lamarin dai ya fi muni ne a birnin Mosul inda aka kashe jami'an 'yan sanda biyar, bayan da suke binciken wani mutum dake kwance a kan titi inda wani bomb dake daure a jikin mutumin ya tarwatse.

Shi kuwa dan takara a zaben Najim al-Harbi, ya mutu ne lokacin da wani bomb da aka dasa a gefen titi a lardin Diyala dake arewacin birnin Baghadaza ya tashi.

Kawo yanzu dai kimanin 'yan takara goma sha hudu ne aka kashe gabannin zaben da aka shirya yi a karshen mako, wanda shine zabe na farko da za'a gudanar a Iraqin, tun bayan da sojojin Amurka suka fice daga kasar.