An daure wani dan adawa a Kuwaiti

Sarkin Kuwaiti
Image caption Sarkin Kuwaiti

An yanke hukuncin daurin shekaru biyar a kan wani fitaccen dan adawa a kasar Kuwaiti bisa zargin cin mutuncin Sarkin kasar, Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah.

A wani jawabi ne ga dubban masu zanga zanga a wajen harabar majalisar dokokin kasar cikin watan Oktoban bara, ya furta cewa ba za a amince sarkin ya mayar da kasar ta Kuwaiti cikin irin mulkin mulaka'u ba.

Kungiyoyin 'yan adawa sun yi barazanar gudanar da zanga zanga a kan tituna idan aka daure shi.

A baya bayan nan dai an daure 'yan adawa, masu rubuta sharhi a shafukan intanet da dama , da ma wasu 'yan siyasa kan irin wannan tuhuma.