'Yansanda a kasar Mexico sun gano wasu gawarwaki 7

Wurin shakatawa na Cancus a kasar Mexico
Image caption Wurin shakatawa na Cancus a kasar Mexico

Jami'an 'yan sanda a kasar Mexico sun gano gawarwakin wasu mutane bakwai, a wani gida dake kusa da fitaccen wurin shakatarwar nan ta Cancu.

Ana dai kyautata zaton kisan nasu bai rasa nasaba da safarar miyagun kwayoyin.

Hukumomin sunce an ga alamu dauri a gawarwakin na maza biyar da mata biyu.

An kuma tsinci gawar wani mutum guda a wani kisa na dabam da aka gudanar a kasar.

A watan da ya gabata ne dai aka harbe wasu mutane bakwai a wani wurin sayar da barasa dake kusa da wurin shakatarwar ta Cancun.

Rahotanni sun ce fiye da mutane dubu saba'in ne aka kashe, tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da wani yaki da take yi da masu safarar miyagun kwayoyi shekaru shida da suka gabata.