An warware rikicin iyaka tsakanin Nijar da Burkina Faso

Shugaba Muhammadu Isoufou na Nijar da kuma shugaban Benin da Blaise Compaore na Burkina Faso
Image caption Shugaba Muhammadu Isoufou na Nijar da shugaban Benin da Blaise Compaore na Burkina Faso

Kotun duniya dake zama a birnin Hague ta warware takaddamar kan iyaka da ake yi tsakanin jamhuriyar Nijer da kuma makwabciyarta Burkina Faso, da suka shafe shekara da shekaru suna ja-in-ja akai.

A shekara ta 2010 ne, kasashen biyu suka garzaya kotun majalisar dinkin duniya a kan shata iyakar dake tsakaninsu, da kasar Faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka ta kasa warwarewa tun a shekarar 1927.

Kasashen biyu sun dauki alkawarin mutunta hukuncin da kotun ta yanke.

Kamfanonin hako ma'adinai da dama sun ce suna gudanar da ayyukansu a kusada guraren da ake takkadamar.

Hukuncin da kotun ta yanke mai sarkakiya, a yanzu ya warware takaddamar da ake yi kan yankin mai tsawon kilomita 380.

Taswira

Rikicin iyakar ya samu asali ne tun shekarar 1927 a lokacin da Faransa wadda ta yi musu mulkin mallaka ta gaza raba kan iyakar.

Shugaban kotun, Peter Tomka, ya ce alakalai sun yanke hukuncinsu ne ta hanayar amfani da matsayar da Gwamna Janar na mulkin mallakar Faransa a yankin yammacin Afrika ya yanke a shekarar 1927, da kuma taswirar yankin da gwamnatin Faransa ta wallafa a shekarar 1960.

Kotun ta duniya da ke shiga tsakani idan kasashe biyu suna rikici kan dokokin duniya, ta yi kira ga kasashen biyu na Afrika da su tabbata sun kula da rayuwar al'ummar fulani da ke tsallakawa tsakanin bangarorin biyu, a duk lokacin da suka yanke shawarar sanya wata alama da za ta raba tsakaninsu.

Yankin kan iyakar tsakanin kasashen biyu dai ya kunshi yanayin sahara da kuma dazuzzuka.

Kamfanonin hakar ma'adinai da dama sun ce suna gudanar da aikace-aikace daban-daban a kan iyakar.

Kasashen biyu sun ce sun yi farin ciki da hukuncin da aka yanke.

Ministan shari'ar jamhuriyar Nijar Marou Amadou wanda ya halarci zaman kotun a Hague, ya shaida wa manema labarai cewa Nijar ta samun karin yanki a hukunci daga bangaren arewa, sannan ta rasa wani yanki daga bangaren kudu.

Sai dai bayanai na uni da cewa hukuncin kotun ya baiwa kasar Burkina Faso karin kasa fiye da Nijar, musamman a yankin kogin Sirba.

Warware rikici

Ana ganin wannan shari'ar da aka yanke za ta iya zama abin koyi ga sauran kasashen Afrika da ke da rikicin kan iyaka tsakaninsu, kan yadda za su iya warware rikicinsu cikin ruwan sanyi.

Kasashen Nijar da Burkina Faso sun yi kokarin warware rikicin tsakaninsu ba tare da sun gurfana a gaban kotun duniyar ba.

A shekarar 2006, shugabannin kasashen biyu sun gana a yankin kan iyaka, domin warware zaman dar-dar da kutsen da jami'an tsaro da na kwastam na kasashen biyu suka yi wa yankin ya haifar.

Kasashen biyu dai a baya sun taba gurfana a gaban kotun ta duniya, a shekarar 2005 kotun ta warware wani rikici tsakanin kasashen Nijar da Benin da kuma a shekarar 1986, kotun ta warware rikicin iyaka tsakanin Burkina Faso da kasar Mali.

A yanzu kasashen na Nijar da Burkina Faso na da watanni goma sha takwas domin aiwatar da hukuncin kotun.

A wasu lokutan, hukuncin kotun ba ya kawo karshen takaddamar iyaka tsakanin kasashe biyu, domin har yanzu kasashen Kamaru da Najeriya ba su kai ga kammala aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke tsakaninsu kan tsibirin Bakassi ba.