Wacece Baroness Thatcher?

Wani Allon adawa da Margret Thatcher lokacin Jana'izar ta
Image caption Wani Allon adawa da Margaret Thatcher lokacin Jana'izar ta

An haifi marigayiya Margaret Hilda Robert a shekarar 1925 a Grantham, wani dan karamin gari dake gabashin Ingila, kuma ita ce karama a cikin 'ya'ya mata biyu da mahaifanta ke da su.

Babanta Alfred na da shagon kayayyakin masarufi kuma yana harkar siyasa.

Ta fara halartar makarantar 'yan mata ta grammar kafin ta tafi jami'ar Oxford, inda ta karanci Chemistry.

Sannan ta samu horo a matsayin lauya a bangaren haraji.

Ta auri bazawarinta, wani hamshakin mai kudi Denis Thatcher kuma sun haifi tagwaye Carol da Mark.

Ita ce Firai ministar Birtaniya da ta kwashe tsawon shekaru a kan mulki, kuma ita ce mace ta farko da ta jagoranci gwamnatin demokradiyya a kasar Turai dake da muhimmanci.

Thatcher ta lashe zabuka uku a jere, inda ta kwashe shekaru 11 a fadar gwamnati ta Downing Street, tun daga watan Mayu na shekarar 1979 zuwa Nuwambar 1990.

Ya aka yi ta shiga siyasa?

Ta biyo babanta wanda dan siyasa ne a karamar hukumar Grantham.

A lokacin da take Oxford a shekarun 1940 ta zama mace ta farko da ta rike shugabancin kungiyar masu ra'ayin 'yan mazan jiya a jami'ar.

A shekarar 1959 tana da shekaru 34 ta samu zama 'yar majalisa daga mazabar Finchley na arewacin London.

A wancan lokacin mata daidaiku ke shiga fagen siyasa.

Ya aka yi ta zamo Firai Minista?

Abubuwa ba su zo wa Mrs. Thatcher da sauki ba, tun bayan da shugaban jam'iyyar conservative Ted Heath ya bata mukamin ministar ilimi a shekarar 1970.

An yi mata lakabi da "Thatcher barauniyar madara"bayan ta yanke shawarar kawo karshen raba madara kyauta ga manyan 'yan makarantar firamare.

A wannan lokacin ba mai kawo wa cewar zata rike mukamin shugabar jam'iyyar bare har ta zama Firai Minista.

Amma bayan jam'iyyarta ta fadi zabe a shekarar 1974, sai aka fara tunanin sauya lale a cikin jam'iyyar.

Kuma wani abu da ya zo da mamaki ga mutane da dama har da ita kanta Thatcher, shi ne doke Mr. Heath din da ta yi wajen zaben shugabannin jam'iyyar.

A shekarar 1979 ne dai likkafa ta yi gaba inda marigayiya Margaret Hilda Thatcher tayi nasarar darewa mukamin Pri Minista a Burtaniya bayan nasarar da jam'iyarta ta samu a babban zaben kasar.

A lokacin da take rike da mukamin Priyi Minista dai marigayiya Magret Thatcher ta yi ta kokarin ganin ta aiwatar da wasu muhimman sauye sauye a bangaren tattalin arzikin kasar.

Kasancewarta mace ta farko da taba darewa mukamin Priyi Minista a Burtaniya, Marigayi Magaret Thatcher dai ta yi kokarin kawo sauye sauye a harkokin siyasar kasar inda ta bullo da wasu sauye na ba-sani-ba-sabo a fannoni dabam dabam, matakin da yasa ta yi kaurin suna har ta kaiga ana kallonta a matsayin shugabar da aka fi kauna kana kuma aka fi tsana a Burtaniya.

Muhimman lokaci a farkon kama mulkinta

Mrs. Thatcher ta lashi takobin farfado da tattalin arzikin Birtaniya dake tangal-tangal, sai dai hanyar da ta bi na yin haka wato ta rage hauhawara farashin kayayyaki da rage kudaden da gwamnati ke kashewa tare da karbo bashi ya jefa kasar cikin matsin da ba a yi hasashensa ba.

Rashin aikinyi ya karu zuwa miliyan uku, a yayin da aka rufe manyan masana'antu da kamfanonin kasar.

Biranen Ingila kuma suka shiga fuskantar bore a shekarar 1981.

Kin janye matakanta kamar yadda Ted Heath ya yi na nufin faduwa a zabe mai zuwa.

A yakin Falklands - ta aika da sojojin ruwa domin sake karbe tsibiran dake kudancin tekun atlantika, wadanda kasar Agentina ta mamaye. Haka kuma an alakanta samun nasararta a zabe na biyu da taimakon da ta samu daga 'ya'yan jam'iyyar Labour dake da bambancin ra'ayi.

Me ya faru a wa'adin mulkinta na biyu?

Image caption Janaizar Margaret Thatcher

Mrs. Thatcher ta sake lashe zabe da gagarumin rinjaye a shkerar 1983, a lokacin da 'yan kasar ke murnar nasarar da ta samu a yakin Falklands.

Sai dai wa'adin mulkinta na biyu ma cike yake da kalubale.

Inda kasar ta fuskanci yajin aikin masu hakar ma'adanai mafi zafi da kuma daukar tsawon lokaci a tarihin Birtaniya.

A watan Oktobar wannan shekarar ne kuma, ana tsaka da yajin aikin kungiyar 'yan tawaye ta LRA ta yi yunkurin kashe Mrs. Thatcher da ministocinta a wani harin bam da ta kai a otel din da jam'iyyar conservative ke yin taro a Brighton.

Tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa a kusan karshen wa'adin mulkinta na biyu, yayin da garanbawul dinta na kasuwa tayi halinta da kuma sayar da kadarorin gwamnati ya fara karfi.

Wa'adin mulkinta na uku fa?

Haka batun yake ma a wannan karon, domin ta samu gagarumin rinjaye a zaben 1987, inda ta kara komawa fadar Downing Street da kujeru mafi rinjaye 102 ga jam'iiyarta.

Hakan yasa ta zama Firai Ministan da ta fi kowa dadewa a gadon mulki, tun bayan Lord Liverpool a farkon karni na 19.

Me ta cimma a rayuwa?

Birtaniya ta sauya fiye da yadda ake zato a karkashin mulkin Thatcher, inda aka rufe manyan masana'antu kuma aka bar kasuwa ta yi halinta.

Akidunta na siyasa har yanzu suna tasiri a siyasar Birtaniya.

Sai dai masu suka na cewa sauye-sauyen sun janyo rabuwar al'umma tare da ruguza ma'aikatun da aka san kasar da su.

Karin bayani