Nicolas Maduro ya lashe zaben Venezuela

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
Image caption Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro

Hukumar zaben Venezuela, ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, da ya nuna cewa shugaban riko, Nicolas Maduro ne ya samu galaba.

Mr Maduro ya samu nasara da sama da kashi hamsin bisa dari na yawan kuri'n da aka kada. inda ya kada abokin takarasa na jam'iyar adawa, Henrique Capriles.

Wannan sakamako shi zai ba Mr Maduro damar ci gaba da gaje kujerar marigayi shugaba Hugo Chavez.

Jami'an hukumar zaben sun ce an kada kuri'ar cikin kwanciyar hankali, sai dai wakilin BBC a birnin Caracas ya ce an dan samu damuwa daga magoya bayan bangarorin biyu, lokacin da suke dakon ganin sun samu cikakken goyon baya.

Shugaban rikon kwarya, Nicolas Maduro,ya yi alkawarin ci gaba da manufofin Mr Chavez.