Capriles ya yi kira da kada a tabbatar da Nicolas Maduro a Venezuela

Image caption capriles zai kalubalanci zaben venezuela

Jagoran 'yan adawa a Venezuela , Henrique Capriles ya yi kira ga hukumar zaben kasar da kada ta bayyana shugaban kasar na riko, Nicolas Maduro a matsayin wanda yayi nasara a zabe, sai an kammala sake kidaya dukkan kuri'un.

Ya ce shi kansa Mr Maduro ya amince a sake kirga kuri'un a jiya, Lahadi.

Mr Capriles ya kuma bukaci a yi zanga zanga ta gama gari a duk fadin kasar idan aka bayyana Mr Maduro a matsayin wanda ya yi nasara.

Tun farko dai Mr Capriles , ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben inda ya sha kaye da dan kankanen rinjaye.

Mr Maduro dai ya samu tazarar kasa da kashi 2 daga cikin dari na kuru'un da aka kada a kan abokin takararsa, amma Mr Capriles ya ce jami'an yakin neman zabensa sun gaano jerin kura-kurai fiye da dubu 3 da aka tafka a lokacin zaben, saboda haka suke bukatar a sake kidayar kuru'un.

Shi dai Mr Maduro, wanda Marigayi Hugo Chaves ya nada a matsayin magajinsa, ya bukaci jama'a da su mutunta sakamakon zaben.

Karin bayani