Mutane dubu bakwai sun bar muhallinsu a jihar Plateau

Wasu jami'an tsaron Najeriya
Bayanan hoto,

Wasu jami'an tsaron Najeriya

Rahotanni daga Najeriya sun ce rikicin kabilanci ya raba 'yan kabilar Jukun kimanin mutane dubu bakwai da muhallinsu, sakamakon fada tsakaninsu da 'yan kabilar Taroh a karamar hukumar Wase dake jihar Pilato.

Fadan dai ya barke ne bayan da aka yi zargin cewa 'yan Kabilar Taroh sun kashe wani dan kabilar Jikun, abun da ya sa 'yan kabilar ta Jikun suka dauki fansa ta hanyar kashe wani dan Taroh.

Hakan kuma ya sa 'yan kabilar ta Taroh kai hari a kan garin Wase Tofa da 'yan Jikun suka fi rinjaye, tare da kona gidaje, abun da ya sa mazauna garin suka fice daga muhallinsu.

An dai soma wannan fada ne tun daga jiya har ya zuwa safiyar yau.

Yanzu haka dai, an tura karin jami'an tsaro zuwa yankin domin kwantad da hankali.

A 'yan makonnin nan dai, an yi ta samun rikicin tsakanin 'yan Kabilar taTaroh da kuma Hausa Fulani a kananan hukumomin Wase da Langtang ta Kudu.