Shugaban Iran ya isa Ghana

Image caption Mahmud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran

Shugaban ƙasar Iran, Mahmud Ahmadinejad ya isa ƙasar Ghana matakin ƙarshe na ziyararsa a ƙasashen yammacin Afurka da ta kai shi Benin da kuma jamhuriyar Nijar.

John Mahama, shugaban ƙasar ta Ghana ne dai ya tarni shugaban Iran a filin saukar jiragen sama na birnin Accra.

Ana sa ran gobe shugabannin biyu zasu tattauna, kuma shugaban Iran zai gabatar da jawabi a jami'ar musulunci dake birnin Accra.

Kafin nan shugaba Ahmadinejad ya ziyarci Benin da kuma jamhuriyar Nijar inda aka sanya hannu akan yarjejeniyoyi a fannoni da dama.