Girgizar kasa ta afka wa Iran

Iran
Image caption Girgizar kasar da aka yi a makon da ya gabata ta yi barna sosai

Wata girgizar kasa mai girman maki 7.8 ta auka wa yankin kudu maso gabashin kasar Iran.

Bayanai da suka fito daga cibiyar binciken yanayin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta fi yin illa ne a wani yanki da ke da nisan kilomita 86 daga birnin Khash dake yankin Sistan na gundumar Baluchistan da ke kan iyaka da kasar Pakistan.

Dogayen gine-gine sun kada a Delhi babban birnin kasar India, yayin da aka ji birbishin girgizar kasar a yankin Gulf da duk fadin yankin gabas ta tsakiya.

Akalla mutane 37 ne suka rasa ransu, yayin da wasu 850 suka samu raunuka a girgizar kasa mai girman 6.3 da ta auka wa yankin kudu maso yammacin kasar ta Iran a ranar 10 ga watan Afrilu.

Girgizar kasar ta shafi yankin da tashar Nukiliyar kasar take a garin Bushehr na kudancin kasar, sai dai jami'ai sun ce ba ta yi barna a tashar ba.

Babu dai labarin samun barna ko rasa rai a wannan girgizar ta baya-bayan nan.

Karin bayani