Ahmadinejad ya kammala ziyara a Nijar

shugaba Ahmadinejad na Iran
Image caption shugaba Ahmadinejad na Iran

A jamhuriyar Nijar yau ne shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadinejad ya kammala wata ziyarar aiki ta yini biyu.

A lokacin ziyarar sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi tsakaninsa da shugaba Muhammadou Issoufou na Nijar.

Yarjeniyoyin sun hada da ta fannin ayyukan noma da ciniki da kuma sufuri.

Yarjeniyoyin ba su shafi ma'adanin Uranium ba, wanda kasashen biyu ke da arzikinsa.

Batun Uranium din na janyo kace nace, ganin yadda wasu kasashe ke zargin Iran da kokarin kera makaman nukiliya, zargin da ita kuma ta musanta tana cewa shirin nukiliyarta na farin kaya ne.

Daga Nijar din bayan sallar Zuhr shugaba Ahmadinejad ya tashi ne zuwa kasar Ghana.

Karin bayani