An gano abubuwan da aka hada bam a Boston

Image caption Jakar da aka sanya bam din a cikinta

A kasar Amurka, hukumomin da ke binciken tashin tagwayen bama-bamai da aka dana a wajen gudun yadda kanin wani na Boston sunce sun ce an yi amfani da wata na'urar girki ne wadda ake kira pressure cooker a turance da wasu karafuna wajen shirya bam din da su ka tashi a garin Boston.

Jami'ai sun ce gano abubuwan da aka hada bam din shine matakin farko na binciken da suke gudanarwa.

Sun ce ta haka dinne za'a san wadanda suka danna bam din.

Mutane sun taru a kungiyoyi a wurare dabam-dabam a Amurka domin jimamin abubuwan da suka faru a Boston a yayinda suke gudanarda adu'o'i.

Har yanzu dai mazauna garin na Boston na ciki kaduwa da ci gaba da nuna makin yadda aka kaiwa taron tseren na Boston hari wanda al'ummar garin ke alfahari da shi.

Masu bincike dai sun ce har yanzu ba a gano wadanda suka kai harin ba, kuma ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko kuma wanda ya amince cewa shine ya kaddamar da harin.

Sai dai mahukunta sun ce sun gano yadda aka hada bam din abun da kuma zai taimaka musu wajen gano wadanda suka danna shi.

Shugaba Obama ya bayyana harin a matsayin ta'adanci. Shugaban kasar dai zai halarci wani taron tunawa da wadanda abun ya rutsa da su a ranar Alhamis.