An samu karin daidaituwar al'amurra-IMF

Christine Lagarde
Image caption IMF ta ce gwamnatoci da bankuna na daukan matakai na rage tafka asara

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya ce an samu karin daidaituwar al'amurra a harkar hada-hadar kudi ta duniya, sakamakon yadda gwamnatoci da manyan bankunan kasashe ke daukar matakai na rage tafka babbar asara.

Sai dai a wani sabon rahoto, asusun na IMF ya yi gargadin cewa idan kuma aka samu cikas a wannan yunkurin, matsalar tattalin arzikin za ta kara yin muni.

Asusun ya ce saka kudin ruwa maras yawa a kasashe masu tasowa na jefa masu zuba jari a cikin hadari, duk da cewar matakin na taimakawa wajen bunkasa ci gaba.

Wakilin BBC ya ce rahoton na cewar idan aka cigaba da samun nasara a fadin duniya wajen yin gyara a bankuna, sannan kuma garan bawul din bai tafiya yadda ya dace, to matsalar za ta iya ta'azzara.

Karin bayani