Nan gaba kadan za a yi janai'zar Thatcher

Image caption Ana jana'izar Margaret Thatcher

Nan gaba kadan ne za yi jana'izar daya daga cikin masu fada aji a cikin jerin Firaministocin Birtaniya da aka taba yi wato, Margaret Tharcher.

Za dai a dauko akwatin gawar ta ta ne a keken dokuna inda za a wuce zuwa majami'ar st. Paul, kuma a cikin girmamawar soji.

Yawancin hanyoyin da za abi an sanya sojoji reras.

Anasaran mutane fiye da dubu biyu ne za su halarci jana'izar ciki har da Sarauniya Queen Elizabeth.

Karin bayani