Landan ta dauki haramar jana'izar Magret Thatcher

Image caption Akwatin gawar Magret Thatcher

Dubban jami'an yan sanda ne zasu kasance a kan titunan London a yau Laraba saboda jana'izar daya daga cikin masu fada aji a cikin jerin Firaministocin Birtaniya da aka taba yi wato Margaret Thatcher.

Za dai a dauko akwatin gawar ta ta ne a keken dokuna inda za a wuce zuwa majami'ar st. Paul, kuma a cikin girmamawar soji.

'Yansanda sun ce suna kyautata tsammanin samun 'yar hayaniya a lokacin jana'izar.

Ana kyautata zaton mutane fiye da dubu biyu da zasu wakilci kasashe dari da saba'in ne za su halarci bikin jana'izar.

Sarauniyar Ingila na daga cikin wadanda za su halarci jana'izar.

Mujami'ar St Paul's a birnin Landa ya dauki haramar jana'izar tsohuwar Fira Ministar kamar yadda aka gudanarda da na wasu tsaffin shugabanin Burtaniya kamar su Nelson da Wellinton da kuma Churchill.

Sama da sojojin dari takwas ne za su gudanarda faretin girmama gawar Laday Thatcher wadda ta tura wasu dakaru tsibirin Falklands a lokacin da aka kasar Argentina ta kwace tsibirin.

Dawakai bakake shida ne zasu za su dauki akwatin gawar ta a wani keke da aka yi amfani da shi a yankin duniya na farko.

A yayinda ake jerin gwano da akwatin gawarta zuwa mujami'ar St Paul's za rika kada kararrawa da rewa wasu wakokin da ita kanta marigayya Thatcher ta zaba kafin a ta rasu.

Shugaban Mujami'ar St. Pauls wanda a baya ya nuna adawarsa a filin game da shirye-shiryen gwamnatin Lady Thatcher ya ce za'a gudanarda da taron jana'izar cikin kanskantar kai.