An sako 'yan Faransan da aka kame a Kamaru

'Yan kasar Faransan da aka kama aka saki
Image caption 'Yan kasar Faransan da aka kama aka saki

An sako 'yan kasar faransan nan bakwai da aka kame a arewacin Kamaru.

Kasashen Faransa da Kamaru duk sun tabbatar da sakin nasu.

Ministan yada labaran Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya shaida wa BBC cewa, mutanen na cikin koshin lafiya kuma babu abinda ya same su.

'Yan kasar Faransan wadanda iyali daya ne da suka hadar da yara hudu, wasu 'yan bindiga ne suka kame su a lokacin da suka kai ziyara gandun daji na Waza da ke arewacin Kamaru.

A wani hoton Bidiyo da aka wallafa a shafin intanet na YouTube, 'yan kungiyar Jama'atu Ahlussunnah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a Najeriya, sun yi ikirarin su ne suka kame su.

Shi ma shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya tabbatar su ne suka kame mutanen.

Karin bayani