An harbe wani dansanda a Boston

Image caption Jami'an tsaro sun yiwa jami'ar kawanya

An harbe wani jami'in dansanda har lahira a harabar wata jami'a a Boston. Lamarin ya faru ne a jami'ar fasaha ta jihar Massachusset.

Hukumomin jami'ar sun gargadi dalibai kan su zauna wuri guda kada su fito, a gefe guda kuma jami'an yansanda sun ce sun yiwa daya daga cikin ginin jami'ar kawanya.

Jami'ar dai na Boston, kusa da inda aka kai harin ranar litinin da ta gabata a lokacin gasar gudun yada kanin wani.

Sai dai kuma babu wata alaka a tsakanin abubuwan da suka faru a birnin.

A wani labarin kuma Hukumar bincike a Amurka wato FBI ta bayyana hotunan wasu mutane biyu da ake zarginsu da hannu a bam din da ya tashi a wajen tseren gudun yada kanin wani na Boston da aka yi a ranar Litinin din da ta gabata.

Hotunan bidiyon sun nuna mutanen sanye da hulunan hana sallah, sa'annan kuma suna dauke da wata jaka da suka rataya a bayansu.

Wani babban jami'i a hukumar, Richard Deslorias ya bukaci jama'a da su samar musu da bayanai.

Karin bayani