Abubuwa sun tsaya cik a Boston

Mutanan da ake zargi da kai hari a Boston
Image caption Mutanan da ake zargi da kai hari a Boston

'Yan sanda a birnin Boston na Amurka, sun ce daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin bam yayin gudun yada-kanin wani ya mutu.

Likitoci sun ce, ya samu raunukan harbin bindiga, kuma anyi artabu sosai tsakaninsa da 'yan sanda.

A halin da ake ciki dai yanzu yan sandan sun kaddamar da gagarumin farautar mutum na biyu da ake zargi wanda suka baiyana a matsayin mai hadarin gaske da kuma ke dauke da makamai.

Yan sandan suka ce su na zargin mutanen sun yi kwacen wata mota ce da suke neman tserewa a lokacin da suka tunkaresu.

An dai umarci mazauna birnin Boston su kasance a gidajensu saboda irin halin da ake ciki.

Karin bayani