An kama Janar Musharraf a Pakistan

Image caption Tsohon shugaban kasar ya dawo daga gudun hijira ne domin tsaya takarar zabe

'Yansanda a Pakistan sun kama tsohon shugaban kasar Pervez Musharraf kuma kotu ta umarci su da su ci gaba da tsare shi na tsawon kwanaki biyu kafin a gurfanar sa shi.

Wasu hotunan talbijin dai sun nuna hotunan Janar Musharraf da wasu 'yansanda a wata kotu a birnin Islamad.

A jiya ne dai wata Kotu ta bada umarnin tsare shi saboda matakin da ya dauka na sanya alkalan kotu daurin talala a watan Maris din shekara ta 2007.

Wani babban jami'in 'yansanda Mohammed Khalid ya ce an kama Janar Musharraf ne a gidansa dake bayan garin Islamabad.

Wani lauyan Janar Musharraf ya ce, alkalin kotu ya umarci 'yansanda da su ci gaba da tsare Mista Musharraf na tsawon kwanaki biyu kafin a gurfanar da shi a gaban kotu. Za'a dai tsare Musharraf ne a gidansa.

A watan da ya gabata dai Janar Musharraf ya dawo daga gudun hijirar da ya yi a inda yake fatar jagorantar jam'iyyarsa ta APML a zaben da za'a gudanar a watan gobe.

Amma a farkon wannan makon ne dai aka ki amincewa da takarar tasa a yankin Chitral, daya daga cikin kujeru hudu da ya nema ya tsaya takara.

Tun a baya dai Janar Musharraf bai yi nasarar tsaya takara a sauran kujeru uku ba.

An dai tsare shi ne yanzu saboda matakin da ya dauka na sallamar alkalan kotun, da kuma babban mai shari'ar kasar a lokacin da ya sanya dokar tabaci a kasar a shekarar 2007.

Har wa yau tsohon shugaban kasar na fuskantar tuhuman kan wasu manyan laifuka da suka hada da cin amanar kasa.

Kungiyar Taliban a Pakistan dai ta sha alwashin halaka tsohon shugaban kasar wanda ya yi juyin mulki a shekara ta 1999.

Karin bayani