An soma bikin fina-finan Afirka

A birnin Yenagoa na jihar Bayelsa dake kudancin Najeriya an soma bikin bada kyaututtuka na gasar fina-finan Afirka karo na tara.

Bikin dai yana samun halartar masu shirya fina-finai da kuma masu fitowa a finai-finai daga kasashe daban-daban na Afurka.

Cikin 'yan shekarun nan dai harkar fina-finai suna cigaba da bunkasa a kasashen Afirka.

Najeriya dai ita ce, kan gaba wajen shirya fina-fnai dake da cibiya a Lagos, kuma harkar tana samar da sana'a ga dimbin matasa.