Satar man fetur a Najeriya na karuwa

Hukumomin Najeriya sun ce sun cafke wani jirgin ruwa dauke da tataccen man fetur ton dubu biyu da dari biyar, wanda aka saato daga kananan hanyoyin ruwa na Okuboto, dake jihar Bayelsa, a yankin Niger Delta.

Rundunar hadin-gwiwa ta JTF a yankin ce ta kaame jirgin ruwan a wani samame da ta kai.

A wata sanarwa da ya aika ma kafofin watsa labarai jami'in hudda da 'yan jarida na rundunar, Laftanar Kanar Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa an kaama jirgin ne a daidai lokacinda barayin man ke kokarin cika tanki na hudu na jirgin ruwan.

Har wa yau kuma an kama wasu budaddun jiragen ruwa masu dan karan gudu guda talatin dake dauke da man fetur din da akai fasa kaurunsa a jahar Delta.

Kamfanonin dake hakar mai a yankin sun ce ana sace gangar mai dubu dari da hamsin a kullum.