Amurka za ta bai wa 'yan adawar kasar Syria tallafi

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya sanar da cewa Amurka zata baiwa 'yan adawar kasar Syria tallafin kayayyakin da basa kisa.

Tallafin dai zai kai dala miliyan dari da ashirin da uku.

Mr Kerry yace wannan sabon gudummuwar za ta zarta taimakon kayayyakin abinci dana magunguna, sai dai kuma bai yi karin bayani ba game da irin tallafin.

Mr Kerry ya bayyana haka ne bayan wani taron Ministocin harkokin waje na kasashe goma sha daya dake kawance da Syria, wanda aka gudanar a Santanbul, babban birnin kasar Turkiya.

An gudanar da tattaunawar ne don bin hanyoyin da zasu taimakawa 'yan adawar wajen samu galaba kan dakarun shugaba Bashar al Assad.

'Yan adawar kasar ta Syria sun bukaci irin taimakon da suke so da suka hada da jiragen yakin da basu da matuka, domin abokan karawarsu dakarun gwamnatin Syria, da kuma karin wasu sansanoni a yankunan kan iyakokin kasar.

Sai dai kungiyar kasashen dake kawance ta kasar Syria sun ce suna da ja game da bukatun.

Mr John Kerry, ya sanar da rubanya tallafin Amurkar ga 'yan adawar, sun kuma hada da samar musu da abubuwa-amma ban da bindigogi- ga 'yan tawayen kasar ta Syria.

Masu aiko da rahotanni sun ce Amurka dai ta gaza bada irin gudummuwar da 'yan tawayen suke fatan samu daga gareta.

Ita dai gwamnatin shugaba Obama ta ce, ta kudiri aniyar dakatar da bayar da makaman ga 'yan adawar, don gudun barazanar da karawa kungiyoyi masu alaka da kungiyar al Qaeda karfi.