Baga: mutane '185' sun mutu

Jahar Borno, arewacin Najeriya
Image caption Jahar Borno, arewacin Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno, arewacin Najeriya sun ce kimanin mutane dari da tamanin da biyar sun hallaka, a wani rikici da ya barke a garin Baga.

Rikicin ya faru ne tsakanin jami'an sojin dake yankin da kuma 'yayan kungiyar Boko Haram.

Hukumomin tsaro a yankin sun ce fararen hula da dama sun rasa rayukansu ne sakamakon garkuwar da 'yan bindigar suka rika yi da su yayin arangamar da aka shafe sa'o'i ana yi tun daga yammacin ranar juma'a.

Lamarin Dai ya sa wasu magidanta da dama sun shige cikin jeji don tsira rayukansu, yayunda wasu suka fada ruwa.

Mazauna yankin sun ce adadin wadanda suka rasun ka iya fin haka, yayinda ake ci gaba da samo wasu gawawwakin cikin dazuka da kuma ruwa.

Wani dan jarida dake cikin tawagar gwamnatin jihar Borno da suka ziyarci garin na Baga a ranar Lahadi ya ce ya ga gidaje, da ababan hawa da dama da suka kone kurmus, yayin da mazauna yankin ne cikin halin kaduwa.

Galibin mazauna garin na Baga dai masunta ne da suka dade suna gudanar da harkokin rayuwarsu a gabar tafkin Chadi.

Garin na Baga dake arewain jihar Borno, ya yi iyaka da kasashen Nijar da Chadi.