An bankado yunkuri kai hari a Canada

Rundunar 'yan sandan Canada
Image caption Rundunar 'yan sandan Canada

'Yan sanda a kasar Canada sun ce sun dakile wani gagarumin yunkurin kai harin ta'addanci da kungiyar alQaeda ta shirya a wani jirgin kasa dake zirga zirga tsakanin biranen Toronto da New York.

'Yan sandan sun ce sun kama mutane biyu, sun kuma tuhume su da laifukka masu nasaba da ta'addanci.

Rundunar 'yan sandan ta ce duk da kasancewa mutane da dama ne zasu halaka ko jikkata idan da an kai harin da ake zargin, amma babu wata alama dake nuna cewa shirin na kan hanyar samun nasara.