Fyade: 'Yan sanda a India sun damke wani mutum

fyade
Image caption Ana yawan yiwa maata fyade a India

'Yan sanda a kasar India sun damke mutum na biyu da ake zarginsa da hannu wajen cin zaracin wata karamar yarinya 'yar shekaru biyar a makon daya gabata a birnin Delhi.

Yanzu haka yarinyar na murmurewa asibiti, kuma cin zarafin ya janyo zanga-zanga a cikin Delhi a karshen mako.

Cin zarafin Maata a kasar India ya zamo babban lamari a cikin kasar tun bayanda gungun matasa suka yiwa wata budurwa fyade a watan Disambar bara.

Karin bayani