Jonathan ya umurci ayi bincike a kan rikicin Baga

boko haram
Image caption 'Yan Boko Haram

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Ebele Jonathan ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan cewa fararen hula da dama sun rasa rayukansu a harin da aka kai a garin Baga na jihar Borno.

Shugaban ya kuma mika jajensa ga al'ummomin da abin ya shafa.

Rahotanni sun nuna cewar mutane akalla 185 aka kashe tare da kuna gidaje da dama sakamakon gwabzawar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Boko Haram.

Jama'a da dama ne suka fice daga garin saboda fadan, inda suka ce a lokacin da suka koma garin, sun ga gawarwaki a jibge a kan tituna.

Wani mazaunin garin na Baga da bai so a bayyana sunansa ba, ya fadawa BBC cewa tuni aka yi jana'izar wasu daga cikin mamatan.

Karin bayani