Mutane da dama sun hallaka a Syria sakamakon wani hari

Rikicin kasar Syria
Image caption Rikicin kasar Syria

Majiyoyin 'yan adawa a Syria sun ce wani hari da dakarun gwamnati suka kai a wani gari dake kusa da birnin Damascus ya hallaka mutane da dama.

Majiyoyin sun ce harin wanda aka kwashe kwanaki 5 ana kaiwa a garin Jidedat al-Fadl, ya yi sanadiyyar rasa rayukan akalla mutane tamanin wadanda galibinsu mata ne da kananan yara, ko da yake akwai mayakan 'yan tawaye da dama a ciki.

Wakilin BBC ya ce wasu hotunan bidiyo da aka sa ayanar gizo sun nuna gawarwaki mutane a jere da aka lullube da bargunan dake dauke da jini.

Babu dai wasu majiyoyi masu zaman kansu da suka tabbatar sahihancinsu.