Baga: an soma kai kayan agaji

Kwamitin da gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya kafa domin tallafawa al'ummar garin Baga ya soma kai kayan agaji ga jama'ar da rikici ya shafa. Rikicin dai ya hallaka mutane 185.

Kwamitin karkashin jagorancin dan majalisar wakilai na yankin Baga, Hon. Isa Lawan yace, ya aika kayan abinci da kuma tufafi domin ga mazauna garin Baga

Tuni dai shima shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan ya umarci ayi cikakken bincike akan musabbabin rikicin na garin Baga.

Rundunar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwa tana cewa, rikicin na Baga ya faru ne ranar Talatar da ta gabata yayin wata arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Boko Haram.

A cewar sojan Najeriya yayin arangamar an kashe 'yan kungiyar Boko Haram su 30, da kuma soja daya, da farar hula shida.

Yanzu haka dai kungiyoyin agaji suna shirin shiga garin na Baga domin kai dauki.