Sojoji sun ce yawan wadanda suka mutu a Baga ba su kai 180 ba

Garin Baga, jihar Borno
Image caption Garin Baga, jihar Borno

A Najeriya, hedkwatar sojojin kasar ta ce mutane 37 ne suka mutu sabanin 185 da ake cewa sakamakon wani tashin hankali da jami'anta suka yi da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Ahlissunna lidda'awati wal Jihad ne a garin Baga dake jihar Borno.

Rundunar ta musanta adadin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a karon farko tun bayan rahoton faruwar artabun mako guda da ya wuce.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan batun.

Ita ma gwamnatin tarayya ta bukaci a gudanar da bincike kan kashe kashen.

A gobe Laraba ake sa ran kungiyoyin agaji, irinsu Red Cross zasu shiga garin na Baga domin kai agaji ga dimbin jama'a ke matukar bukata.

Karin bayani