An sace limaman kiristoci biyu a Syria

Limamin Kirista a kasar Syria
Image caption Limamin Kirista a kasar Syria

Wasu 'yan bindiga a arewacin kasar Syria sun yi awon gaba da wasu limaman kiristoci biyu wanda suka fito daga kan iyakar Turkiya.

Limaman dai na kan hanyarsu ta zuwa majami'unsu dake birnin Aleppo.

Kafafen yada labaru na gwamnatin Syria sun bayyana mutanen da suka sace Limaman Kiristocin a matsayin 'yan ta'adda.

Wadannan Limaman Kiristocin sune Yohanna Ibrahim, wanda shine shugaba cocin Orthodox a birnin Aleppo da kuma Boulos Yaziji, shugaban cocin Greek a birnin.

A kwanakin baya ne dai daya daga cikin Limaman wato Bishop Ibrahim, yayi hira da sashin larabci na BBC, inda ya bayyana cewa dukkanin bangarori biyu a Syria na da alhakin tashe tashen hankulan da ake fuskanta.

Bishop din na mai cewa babu wanda zai iya tilastawa mabiya addinin kirista daukar makamai, amma akwai wasu daidaiku dake daukar makaman, domin kare gwamnati, kana wasu kiristoci na daukar makaman tare da hadin gwiwar 'yan adawa.