Israila ta zargi Syria da amfani da makamai masu guba

Ana wanke makamai masu guba
Image caption Ana wanke makamai masu guba

A karo na farko Israila ta zargi Syria da amfani da makamai masu guba akan dakarun 'yan tawayen kasar.

Jagoran sashen leken asiri na sojojin Israila, Birgadiya Itai Baron ya shaidawa wani babban taro akan harkokin tsaro cewar hakan ya faru a karo daban daban, ciki kuwa har da wani hari da aka kai ranar 19 ga watan Maris.

Ya ce shaidar da ake da ita ta hada da hotunan da ke nuna wadanda abun ya shafa suna fama da alamun rashin lafiya na iska mai kashe lakkar jiki, kuma da alama sinadaran da aka yi amfani da su suna rukunin gubar Sarin ne.

Ana ci gaba da nuna damuwa akan yiwuwar amfani da dumbin makamai masu gubar da Syria ta ke da shi a wannan rikici da ya shiga shekara ta ukku.