An kaddamar da kwamitin sasantawa da Boko Haram

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da kwamitin sasintawa tare da 'yan kungiyar nan ta jama'atu ahlus Sunna Lid Da awati wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

Kwamitin mai wakilai 27 da gwamnatin ta kafa bayan Shugaban kasar ya ga na da dattawan arewacin kasar a kwanan baya, zai tattauna da shugabannin kungiyar ne da nufin lalubo hanyar lumana ta kawo karshen tashen hankalin da yaki ci yaki cinyewa a arewacin kasar.

A jiya ne shugaban Najeriyar ya sanar da karin sunan Barr. Aisha Wakil a cikin membobin kwamitin.

Taron kaddamar da kwamitin ya zo ne kasa da mako guda da wata mummunar arangama da aka yi tsakanin sojoji da wasu da ake zargin 'ya'yan kungiyar ne a garin Baaga na jihar Borno inda rahotanni ke cewa an kashe mutane kimanin dari biyu.

Sai dai hedkwatar sojojin kasar ta ce mutane 37 ne suka mutu sabanin 185 da ake cewa.

Rundunar ta musanta adadin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a karon farko tun bayan rahoton faruwar artabun mako guda da ya wuce.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan batun.

Ita ma gwamnatin tarayya ta bukaci a gudanar da bincike kan kashe kashen.

A gobe Laraba ake sa ran kungiyoyin agaji, irinsu Red Cross zasu shiga garin na Baga domin kai agaji ga dimbin jama'a ke matukar bukata.

Karin bayani