Mutane akalla 100 sun mutu a Bangladesh

Bangladesh
Image caption Bangladesh

Jami'ai a Bangladesh sun ce mutane kimanin dari suka mutu sakamakon rugujewar wani bene mai hawa takwas a wajen Dhaka, babban birnin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ayyukan ceto na gudana, yayinda wasu na can danne cikin baraguzan ginin.

Ginin benen ya kunshi kampanonin yin tufafi da bankuna da kuma shaguna.

A na yawan samun wannan matsala ta rushewar gine gine a Bangladesh, kuma 'yan sanda sun ce an sanar da wadanda suka mallaki gidan benen cewa wurare da dama na tsattsagewa a jikinsa.

Wannan hadari ya kara sa jamaa suna duba irin matakan kiyaye lafiyar jamaar da ake dauka a masa'anatun saka kayayyaki Bangladesh, wadnda suke fitar da kayan sawa zuwa kasashen turai da Amurka.

A watan nuwamban da ya wuce, mutane fiye da dari da goma ne suka rasa rayukansu a lokacin da wata gobara ta kama a wata masana'antar kayayyaki da ke bayan Dhaka babban birnin kasar.