'Yan Canada sun musanta zargin kai hari

An dai kai mutanen biyu kotu ne a Montreal da Toronto
Bayanan hoto,

An dai kai mutanen biyu kotu ne a Montreal da Toronto

A Canada, mutane biyu da ake zargin yan kungiyar Al Qaeda ne da kuma shirya kai hari a kan wani jirgin kasan fansinja sun kalubalanci tuhumar da ake musu.

Lauyan Read Jaser dai ya musanta tuhumar da ake ma wanda yake karewa.

Chiheb Essaghaier da Raed Jaser sun bayyana a Kotu a Montreal ne da kuma Toronto.

A tuhume su ne da shirya kissa da kuma kawo cikas ga harkokin sufuri a kasar a madadin wata kungiyar ta'ada.

Ana dai zarginsu ne da shirya kai hari wa wani jirgin kasa a Toronto.

Essaghaier a wata dan gajeren bayani da yayi da harshen farasanci ya ce masu shigar da kara ba su da cikakkun shaidu cewa yana da hannu a lamarin.

Har wa yau dai yaki amincewa da wani lauyan da kotun ta ce ya wakilce shi.

A wata babbar unguwar musulmi da ke arewa masu gabashin Toronto, musulmai da dama sun nuna rashin jin dadinsa ga labarin shirya kai harin.

Sheik Yusuf Bada na kungiyar gidauniyar addinnin Islama na Toronto ya shaidawa BBC cewa al'ummarsa na da kya-kyawar alaka da hukumomi a kasar.

'Yan sanda sun fara binciken shirin kaddamarda harin ne bayan wasu bayanai da suka samu daga al'ummar musulman kasar.