Shugaba Napolitano na Italiya ya bukaci Enrico Letta ya kafa gwamnatin hadaka

Shugaba Giorgio Napolitano na Italiya
Image caption Shugaba Giorgio Napolitano na Italiya

Shugaban kasar Italiya Giorgio Napolitano ya bukaci mukaddashin shugaban jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayin sauyi wato centre left democratic party Enrico Letta ya kafa gwamnatin hadaka wadda za ta kunshi dukkanin jam'iyu don hadin kasa.

Ana fatan hakan zai kawo karshen kiki-kakar da ta dabaibaye siyasar kasar ta Italiya tsawon watanni biyu tun bayan zaben da aka gudanar wanda bai ida kammaluwa ba.

A can baya dai Mr Letta ya taba kasancewa mamba a reshen matasa na jam'iyyar masu ra'ayin rikau yayin da kawunsa kuma na hannun daman tsohon Firaministan Italiyan, Silvio Berlusconi ne.