Hukumomin agaji sun isa Baga

Hukumomin agaji a Najeria sun isa garin Baga domin kai dauki ga mutanen da suka tagayyara bayan tashin hankalin da ya auku tsakanin jami'an tsaro da wasu da ake zargin 'yan kungiyar nan ce da aka fi sani da Boko Haram.

Rahotanni dai na nuna cewa mutane sama da dari da tamanin ne, da suka hada da mata da kananan yara suka mutu, wasu sama da haka jikkata a tashin hankalin, duk da yake sojin Nijeriya na cewa mutane talatin da bakwai ne suka mutu, a wannan rikici da aka ce ya faro tun ranar Talatar makon jiya.