Sama da mutane 200 sun mutu a Bangladesh

Bangladesh
Image caption Bangladesh

Hukumomi a Bangladesh sun ce a yanzu haka mutanen dari da hamsin ne suka rasa rayukansu sanadiyar ruftarwar wani gini mai hawa takwas a wajen garin Dhaka a ranar Laraba da safiya.

Masu aikin ceto sun kwashe daren jiya sun neman wadanda suke raye a buraguzan ginin.

Sun dai fuskanci matsala saboda basu da isasun kayan aikin da zai taimaka musu wajen aikin ceton.

Masu aikin sa kai da dama ne dai sun taimaka inda suka rika amfani da hanayen su wajen kwashe karafuna da duwatsu da suka rufe mutane.

Adadin wadanda abun ya rutsa da su ya karu ne matuka cikin dare. Duk da haka ana kyautata zaton akwao daruruwan mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.

Masu aikin ceto dai sun ce suna jin karar ihun mutane a cikin ginin da ya rushe suna ihu a kawo musu taimako.

Ginin dai ya dauke ne wasu masana'antu sarrafa kayan sawa da baki da kuma wasu shagunan kasuwanci.

Rahotanni dai sun ce ginin ya fara tsagewa ne tun kafin ya rushe a ranar Laraba amma sai masu kulla da ginin suka nuna halin ko in kula kuma suka shaidawa ma'aikata a wajen cewa kada su damu.