An kashe mutane 7 a artabu a Gashua

Image caption Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohin dake fame da hare-haren kungiyar Boko Haram

Akalla mutane 7 sun rasa rayukansu sakamakon aratabun da aka yi tsakanin Jami'an tsaro da kuma 'yan bindiga da ake zargin 'Yan Boko Haram ne a garin Gashua dake Jihar Yobe.

An dai kusan wayar gari ana misayar wuta a arangamar da akayi a daren jiya Alhamis.

Kakakin rudunar tsaro na JTF din a jihar Yobe, Lt Eli Lazarus a wani sako da ya aikowa BBC ya ce yan sanda biyu sun rasu sannan kuma yan Boko Haram biyar su ma sun mutu a misayar wutar.

Lt Lazarus ya kara da cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne su ka kai hari a sansanin sojin da ke Gashua da kuma Ofishin 'yan sanda a garin.

A cewar sanarwar, abubuwan da aka gano bayan artabun sun hada da: Mota kirar Toyota, da Peugeot 406, da bindiga kirar AK 47 guda daya.

Wasu mazauna garin dai sun shaidawa BBC cewa sun kwana ne suna jin karar harbe-harbe a daren jiyan.

Tuni dai gwamnatin jihar yoben ta sanya dokar hana zurga zurga a garin na Gashau daga karfe bakwai na safiyar yau zuwa karfe daya na rana.

Ta ce kuma jama'ar garin na Gashu'a za su iya fita harkokinsu daga karfe daya na rana zuwa karfe shida na maraice, lokacin da dokar hana zurga zurga da ke aiki a gabaki dayan jihar za ta fara aiki.

An yi awon gaba da DPO a Bama

Rahotanni daga garin Bama a jihar Borno da ke makwabtaka da jihar Yoben na cewa, wuta na can na ci a wasu yankuna na garin bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani babban jami'in 'yan sada a garin.

Rahotanni sun ce 'yan bindiga sun yi awon gaba da DPOn.

Jami'an tsaron da muka tuntuba sun ce sun samu labarin aukuwar lamarin, amma ba su kai ga tantance hakikanin abinda ya faru ba tukunna.

Za kuma su yi karin bayani nan gaba.