Ana kamfe din yakar Kyanda a Ingila

Image caption An durfafin yara miliyan daya don rigakafi a Ingila

Yara 'yan makaranta miliyan daya ne a Ingila aka durfafa a kamfe na allurar rigakafi don yaki da sake bullar cutar kyanda.

Jami'an lafiya sun yi gargadin cewa makamanciyar annobar da ta barke a Swansea dake Wales zai iya faruwa a ko ina.

Akwai damuwa da aka nuna cewa yaran wannan zamanin na da karancin kariya daga cutar kyanda saboda tsoron allurar da aka yi da ake kira MMR, shekaru goma da suka wuce.

Cutar dai kusan an kawar da ita a Ingila a shekarar 1990 amma an samu wadanda suka kamu kusan dubu biyu a bara.

Karin bayani