Hare hare a arewa maso gabashin Najeriya!

Maiduguri
Image caption Maiduguri

Hukumomin 'yan sanda a Jihar Borno, a arewa maso gabashin Nigeria sun tabbatar da cewar an kai wani hari da ranarnan a garin Bama da ke cikin Jihar.

Rahotanni daga garin na Bama na cewar wasu 'yan bindiga ne da ba a san ko su wanene ba suka kaiwa 'yan sanda hari ciki har da DPOn 'yan sanda na karamar hukumar.

Wasu mazauna garin sun ce an banka wuta a kasuwar garin tare da gidajen dake kusa da wurin da lamarin ya faru.

A wani labarin kuma yawancin mazauna garin Gashua a jahar Yobe sun kwana basu runtsa ba, saboda karar harbe-harben bindiga sakamakon fafatawa tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram.

Yanzu dai an kara tsaurara dokar zirga-zirga a garin na Gashua, kuma rahotanni na cewa, an kashe akalla mutane bakwai a arangamar da aka yi a garin.

Karin bayani