Gini ya rufta a kan dalibai a Taraba

Image caption Najeriya dai na fama da matsalar ruftawar gine-gine

A jihar Taraba dake arewacin Najeriya wani ginin dakin rubuta jarabawa mai hawa daya na WAEC ya rubta akan daruruwan dalibai dake rubuta jarabawar.

Wannan al'amari dai ya auku ne a garin Marabar Ba-isa dake karamar hukumar Donga inda bayanai ke cewa, an samu asarar rayuka da kuma jikkata.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani game da adadin mutanen da suka rasa rayukansu.

Bayanai sunce rufin ginin da kuma ginin sun rufta ne a kan daliban a lokacin da suke rubuta jarabawa.

Rahotanni dai sunce ginin ya rufta ne a lokacin da ake ruwan sama mai karfi, amma dakin rubuta jarabawar ne kawai ya rufta.