An kaddamar da hari a jihar Adamawa

Rahotanni daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a karamar hukumar Mayo Belwa mahaifar gwamnan jihar a daren jiya.

Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da irin barnar da aka samu ba sakamakon harin,

Kakakin 'yansandar jihar, Ibrahim Muhd ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.

Mazauna garin dai sun ce sun ji karar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa a wuraren ofishin yansanda da gidan yari da kuma wasu Bankuna.