Mutane 3 ne suka mutu a harin Adamawa

Shugaban Kungiyar da ake kira Boko Haram
Image caption Shugaban Kungiyar da ake kira Boko Haram

An kashe akalla mutane ukku, wadanda suka hada da jami’an ‘yan sanda biyu, a wani harin da ‘yan bindiga suka kai zuwa garin Mayo Belwa na Jihar Adamawa. ‘Yan sanda da mazauna garin sun ce an kai harin ne a jiya cikin dare.

‘Yan bindigar sun kaiwa ofishin ‘yan sanda da wasu bankuna biyu dake garin hari, inda suka kuma jiwa mutane biyu raunuka. Kawo yanzu dai babu wanda aka kama dangane da kai harin, amma ‘yan sanda na can na sintiri a garin.

Wannan ne dai hari na baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka kai a Jihar Adamawa. Makonni biyar da suka gabata sun kai wani harin da ya fi wannan muni a garin Ganye, inda suka kashe akalla mutane 28. A farko wannan watan ma sun kai hari a karamar hukumar Madagali inda suka kashe akalla mutane 14, wadanda suka hada da masu gadin gidan mataimakin gwamnan jihar Bala James Ngilari.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda jihar Adamawan Mohammed Ibrahim ya shedawa BBC cewa mutane ukku ne aka kashe a harin da aka kai jiya da daddare a garin na Mayo Belwan. Yace biyu daga cikin wadanda aka kashen jami’an ‘yan sanda ne, mace da namiji, wadanada ‘yan bindigar suka farmawa kafin su ankara.

Yace amma ‘yan sanda sun maida martani, sun harbi daya daga cikin wadanda suka kai harin, sai dai babu wanda suka kama daga cikinsu.