An dakatar da mai shari'a Talba

njc
Image caption Ginin hukumar sa'ido kan shari'a a Najeriya (NJC)

Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a Najeriya NJC, ta bada sanarwar dakatar da mai shari'a Abubakar Mahmud Talba na babbar kotun birnin tarayya na Abuja daga aikinsa, har na tsawon shekara guda ba tare da biyansa albashi ba.

An dakatar da alkalin daga aikinsa ne, sakamakon binciken da hukumar ta yi, inda ta ce ta gano cewa baya gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Shi dai Alkali Talba, shi ne ya yanke hukunci daurin shekaru biyu ko kuma tarar naira dubu dari bakwai da hamsin a kan wani jami'in hukumar kula da Pansho ta Najeriya da aka samu da laifin yin sama da fadi da dubban miliyoyin nairori na 'yan fensho.

Hukumar ta kuma gargadi mai shari'a Okechukwu okeke da zai yi ritaya a watan Mayu mai zuwa, da ya mayar da hankali wajen irin hukunce-hukuncen da yake yanke wa.