Gobara a asibitin masu tabun hankali a Rasha

Jami'ai a kasar Rasha sun ce akalla mutane 36 suka rasu sanadiyar wata gobara a wani asibitin masu tabun hankali a yankin Moscow.

Gobarar dai ta fara ne a daren jiya a kauyen Ramenskiy.

Yawanci dai wadanda gobarar ta rutsa da su marasa lafiya ne, kuma akwai fargabar cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu za su karu.

Ana dai binciken musababin gobarar amma akwai rahotannin dake cewa wutan latarki ne ya janyo ta. Gobarar dai ta fara ne a bangaren ginin da ake ajiye masu tabun hankalin da suka yi tsakanani.

Ya zuwa yanzu dai ma'ikatan kwana-kwana sun ciro gawawwaki goma sha biyu ne daga ginin. Wani jami'i ya ce tagogi dakunan asibiti na dauke ne da karafuna abun da kuma ya hana marasa lafiya fita daga dakunansu.

Ya ce da dama daga cikinsu a same su ne a kwance a kan gadajensu.

Ana dai ganin asibiti na dauke ne da mutane arba'in da daya.