'Syria na amfani da makamai masu guba'-Cameron

Pira ministan Burtaniya, David Cameron ya ce karin hujjojin da ake samu cewa gwamnatin Syria na amfani da makamai masu guba, za su iya kasancewa laifufukan yaaki.

Ya ce akwai yiwuwar gwamnatin Syria na da hannu a wannan al'ammari, kuma ya amince da matsayin shugaba Obama na cewa ya kamata kasashen duniya su kafa hujja da wannan batu, domin daukan karin matakai a kasar ta Syria.

Wakilin BBC ya ce "mataimakin ministan harkokin wajen Syriar, Fayzak Makdad, ya yi watsi da zargin da aka yi cewa sojojiun gwamnati sun yi amfani da makamai masu guba, ko kuma Syria ta hana Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da bincike a kan al'amarin a cikin kasar".

A halin da ake ciki kuma, masu fafutika na 'yan adawa a Syriar sun ce an yi mummunan artabu a Arewacin birnin Damascus inda sojojin gwamnati ke amfani da manyan makamai a kan 'yan tawaye.

Karin bayani