'An biya Boko Haram kuɗin fansa'

Image caption An dai yi garkuwa da 'yan kasar Faransan ne a watan Fabrairu

Rahotanni daga Najeriya sun ambato wani rahoto na gwamnati mai kunshe da bayanan sirri yana cewa an biya kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram kudin fansa da suka kai dala miliyan uku kafin ta saki Faransawan da ta yi garkuwa da su.

An dai saki Faransawan ne a makon da ya gabata a Kamaru kusan watanni biyu bayan an yi garkuwa da su.

Rahoton gwamnatin Najeriya mai bayanan sirrin dai bai bayyana wanda ya biya kudin fansan ba, wanda kuma ya kai ga sakin iyalan faransawan nan sun bakwai a makon da ya gabata.

Bayanan sirrin da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce ya gani ya bayyana cewa an baiwa kungiyar Boko Haram sama da dalan Amurka miliyan uku ne.

A watan Febrairun din daya gabata ne dai aka yi garkuwa da 'yan kasar Faransan a lokacin da suke yawon shakatawa a wani gandun namun daji dake arewacin Kamaru.

A lokacin da aka sake su gwamnatin Faransa da na Kamaru sun musanta cewa sun biya kudin fansa.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya bata mayar da martani game da wannan labari ba.

Masana dai na ganin idan har ya tabbata cewa an biya kungiyar Boko Haram kudin fansan, toh zai karfafa su sosai musamman wajen siyan makamai.

Kusan mako guda kenan ake fama da tashin hankali a kusan kullum a arewacin Najeriya inda jam'an tsaro ke fuskantar hare-hare.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa kusan fararen hula dari biyu ne saka rasa rayukansu sanadiyar tashin hankalin.

Duk wannan dai na zuwa ne a yayinda gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamitin domin sasantawa da kungiyar ta Boko Haram.

Karin bayani