An zargi tsoffin 'yan tawaten Ivory Coast

Image caption Ana zargin tsoffin yan tawayen da fasa kauri

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi tsoffin 'yan tawayen Ivory Coast wadanda suka taimaka Shugaba Alassane Ouattara ya dare mulki.

Majalisar ta zarge su ne da laifin fasa-kwauri da kuma kwace.

A wani rahoto da suka gabatarwa Kwamitin Sulhu, wasu kwararru masu aiki da Majalisar ta Dinkin Duniya sun ce tsoffin kwamandojin 'yan tawayen, wadanda ke rike da mukaman hafsoshin soji a yanzu ba su yi watsi da dabi'unsu na kama-karya ba.

Rahoton ya ce wani katafaren hadin-gwiwa a fadin kasar ta Ivory Coast ta fuskar soji da tattalin arziki yana yin tarnaki ga yunkurin gwamnati na magance kwasar albarkatun kasa ta haramtacciyar hanya.